ABNA24 : Firaministan Falasdinu, Mohammad Shtayyeh, ya ce matakin dawo da tallafin na Amurka abu ne mai kyau, kuma zai iya bude wani babi na karfafa alaka da gwamnatin Washington.
Tallafin da Amurka na Amurka ya kai dala miliyan 235, wanda ya kunshi miliyan 150 ga shirin MDD na kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinu, sai kuma dala miliyan 75 da Amurka za ta zubawa domin ayyukan ci gaban tattalin arzikin yankunan falasdinawa, sai kuma dala miliyan 10 na shirin karfafa zaman lafiya.
A ranar 7 ga watan ne, shugaba Joe Biden ya sanar da dawo da tallafin da Amurka ke bai wa Falasdinawa, shirin da tsohon shugaban kasar Donald Trump, ya dakatar a shekaru uku da suka gabata.
Saidai tuni Isra’ila, ta bakin jakadanta a Amurka ta nuna jin takaici da kuma kin amincewa da bai wa Falasdinawa tallafin, har sai an kawo gyara ga hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa musamman akan abunda ya shafi nuna kin jinin Isra’ila.
342/